DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar Dattijai ta mikawa shugaba Tinubu kudirin sake fasalin haraji domin amincewa

-

Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa.

Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a lokacin wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata.

Google search engine

A shekarar da ta gabata ne shugaba Tinubu ya gabatar da kudirori hudu kan tsarin haraji domin tantancewa. Bayan dogon muhawara, majalisun biyu sun amince da su.

Sanata Adaramodu ya tabbatar da cewa majalisa ta kammala aikinta kuma yanzu ta mika kudirin zuwa fadar shugaban kasa don daukar mataki na karshe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Saurayi ya gaggabe wa budurwarsa hakora shida a Legas

Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa...

Majalisar dattawan Nijeriya ta ba shugaban NNPCL wa’adin mako 3 kan batan Naira tiriliyan 210

Majalisar dattawan Najeriya ta bai wa Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, wa’adin makonni uku domin ya bayyana cikakken bayani kan inda...

Mafi Shahara