Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin nasarawa za ta gina sansanonin tsaro a kowane yankin Sanata na...

Gwamnatin nasarawa za ta gina sansanonin tsaro a kowane yankin Sanata na Jihar

Saboda yawaitar matsalar rashin tsaro, Gwamnatin Jihar Nasarawa ta bayyana shirinta na kafa sansanonin tsaro a kowane daga cikin yankunan sanatoci guda uku na jihar, domin kara inganta zaman lafiya da tsaro.

Daily Nigerian ta ruwaito kwamishinar kudi da tsare-tsare ta jihar, Munira Abdullahi, na bayyana haka yayin taron jin ra’ayin jama’a kan kasafin kudin yankin Nasarawa ta Arewa da aka gudanar a karamar hukumar Keffi, ranar Laraba.

Munira, wadda Babban Sakataren ma’aikatar kudi, Polinus Wahe, ya wakilta, ta ce matakin ya biyo bayan korafin jama’a kan bukatar karin tsaro a yankunansu.

Gwamnatin ta ce wannan shiri na daga cikin dabarun da take dauka domin tinkarar kalubalen tsaro a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata