Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMajalisar wakilan Nijeriya ta kwato harajin Naira bilyan 86.5 da ba a...

Majalisar wakilan Nijeriya ta kwato harajin Naira bilyan 86.5 da ba a saka asusun gwamnati ba

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin dukiyar al’umma ya gargadi kamfanonin hakar mai 13 da su bayyana a gabansa domin amsa tambayoyi kan binciken da ake yi na rashin saka makudan kudaden haraji a asusun gwamnatin tarayya ko kuma su fuskanci takunkumi.

Kwamitin na zargin gwamnati na bin kamfanonin bashin kimanin dala miliyan 456.95 wanda ya kai Naira biliyan 731.12, na kudaden shiga da ba su saka wa gwamnati ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar wakilan Nijeriya Mista Akin Rotimi ya fitar, majalisar ta ce duk da gayyatar kamfanonin da kuma sanarwar da aka buga a jaridun kasar, kamfanonin sun ki bayyana a gaban kwamitin.

Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban kwamitin, Bamidele Salam yana cewa, duk kamfanin da ya kasa bayyana zai fuskanci fushin doka.

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin ya sanar da kwato karin Dala milyan 15.7, kimanin Naira bilyan 25 daga wasu kamfanonin mai, wanda ya sa adadin kudaden da aka kwato ya kai Naira bilyan 86.5.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata