Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiZugacoin da Samzuga GPT yaudara ce kar wanda ya saka kudinsa -...

Zugacoin da Samzuga GPT yaudara ce kar wanda ya saka kudinsa – Sakon SEC ga ‘yan Nijeriya

Hukumar SEC mai kula da hada-hadar hannun jari ta gargadi ‘yan Nijeriya kan zuba jari a kudin badini na Zugacoin da Samzuga GPT.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa masu tallata wadannan kudaden na kiripto ba su da rajista yin aiki ta kowace hanya a kasuwar hannayen jari ta Nijeriya.

Ta shawarci jama’a da su guji yin siya ko tallata Zugacoin da Samzuga GPT inda ta ƙara da cewa duk wanda ya saka hannun jari a cikin tsarin ya sani cewa ya yi hakan ne bisa radin kansa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata