Cibiyar bayar da agaji ta Sarki Salman na kasar Saudiyya (KSrelief) ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa da wata kungiya don gina rijiyoyin burtsatse 78 masu amfani da hasken rana a jihohi 10 Nijeriya.
Wata sanarwar ta ce ana sa ran shirin zai samar da ruwan sha ga kusan mutane 733,350, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Mataimakin babban mai kula da ayyuka da shirye-shirye na Cibiyar KSrelief, Engr Ahmed bin Ali Al-Baiz ya sanya hannu kan yarjejeniyar a hedkwatar KSrelief da ke birnin Riyadh.
Ta ce yarjejeniyar tana da nufin samar da tsaftataccen ruwan sha ga mutane da dabbobi, da kuma inganta samar da tsaftatattun ruwan sha a yankunan karkara.