Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBabu ta yadda Tinubu zai ci zaben 2027 - Nasiru El'rufai, tsohon...

Babu ta yadda Tinubu zai ci zaben 2027 – Nasiru El’rufai, tsohon gwamnan Kaduna

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba ta yadda Shugaba Tinubu zai sake cin zabe a shekarar 2027 domin abu ne da ba zai yiwu ba.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa X a ranar Alhamis, El-Rufai, wanda jigo ne a jam’iyyar SDP, ya bayyana cewa al’umma sun gaji da mulkin jam’iyyar APC, kuma sun cire tsammani kan gwamnatin yanzu.

Nasiru El-Rufai ya ce duk wanda ke tunanin za a sake zaben Shugaba Bola Tinubu yana rayuwa ne a wata ƙasa daban, ba Najeriya ba, domin babu wata hanya da za ta kai shi ga nasara.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata