Alhazan biyu daga jihar Kaduna sun mayar da kayayyaki da kudade da aka manta da su yayin aikin hajji, da darajarsu ta haura naira miliyan 14.
Shafi’u Abdul’aziz daga Lere ya samu jakar kudi da wayoyi a Harami, mallakin wani dan Mali, ya kai ta ga hukumar alhazai.
Haka kuma, Alhaji Sha’aban Sidi daga Igabi ya mika wata jaka da ya samu a bandaki, wacce ta ƙunshi kimanin naira miliyan 4, mallakin wani dan Aljeriya.
Hukumar alhazai ta Kaduna ta yaba da gaskiya da amana da alhazan suka nuna, tana mai cewa hakan abin koyi ne ga alhazai na duniya kamar yadda shafin Facebook na Hajj Reporters ya tabbatar.
