Olufemi Soneye, mai magana da yawun kamfanin NNPCL, ya ajiye aikinsa bayan watanni 20, yana mai cewa ya yanke shawarar mayar da hankali kan iyalinsa da wasu al’amura na rayuwa.
Jaridar Punch ta Ambato Sonoye a cikin sanarwar da ya wallafa a shafin Facebook, na cewa ya yi alfahari da gudunmawar da ya bayar wajen sauya fasalin NNPCL, kuma zai ci gaba da kasancewa jakadan kamfanin a duk inda yake.
Kafin nadinsa a 2023, ya yi aiki a kafafen labarai na cikin gida da na ƙasashen waje, kuma ya rike manyan mukamai a ƙungiyoyin NUJ da NABJ. A 2024 da 2025, an karrama shi da lambar yabo ta “Mai magana da yawun shekara” daga NIPR.
