Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yi alhinin rashe-rashe da aka samu Konduga da Kano, ya...

Tinubu ya yi alhinin rashe-rashe da aka samu Konduga da Kano, ya umarci NEMA ta kai dauki cikin hanzari

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai a Konduga, Jihar Borno, yana mai bayyana shi a matsayin rashin imani da tsoro.

A wata sanarwa da jaridar Punch ta samu wadda mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya nuna damuwa da jimamin asarar rayuka, tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar.

Ya bukaci hukumomin tsaro su kara azama wajen dakile ayyukan masu tayar da kayar baya, tare da umartar NEMA ta kai dauki ga wadanda harin ya rutsa da su.

Tinubu ya kuma bayyana alhininsa kan fashewar da ta auku a wata masana’antar karafa a Kano da ta yi sanadin mutuwar mutane biyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata