Gwamnatin jihar Kebbi ta nuna rashin jin dadinta kan kalaman da tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, SAN ya yi, inda ta zarge shi da sanya siyasa cikin al’amuran tsaro.
Malami dai ya yi zargin cewa an halaka akalla mutane 200 a wani harin ‘yan bindiga da suka kai kwanan nan a Masarautar Zuru, ikirarin da gwamnatin jihar ta yi watsi da shi ta ce kalamai ne kawai na son rai.
A jawabansu da suka fitar kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Yakubu Ahmad da kuma mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai Yahaya Sarki, sun bayyana kalaman Abubakar Malami a matsayin shaci fadi inda suka yi zargin cewa yanayinsu ne domin samun karbuwa a siyasance.
Kwamishinan ya bayyana cewa daga shekarar 2015 zuwa 2023,Malami ya rike daya daga cikin manyan ofisoshi a Nijeriya a matsayin Atoni Janar a karkashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, amma duk da haka a lokacin, Zuru da sauran sassan jihar Kebbi sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga, ba a taba samun labarin ya kai ziyara ko aiko wasika domin yin jaje ko ta’aziyya ba.