Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHukumar EFCC ta kama wani tsohon jami'i a kamfanin NNPC bisa zarginsa...

Hukumar EFCC ta kama wani tsohon jami’i a kamfanin NNPC bisa zarginsa da almundahanar dala biliyan 7.2

Jami’an hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya tu’annati, sun kama tsohon babban jami’in kudi na kamfanin NNPCL Umar Isa, bisa zarginsa da almundahanar kudin da suka kai dala biliyan 7.2 na gyaran matatun mai na Kaduna, Warri da Fatakwal.

Haka kuma EFCC ta kama Jimoh Olasunkanmi, tsohon manajan darakta na matatar mai na Warri, da manajan daraktan matatar na yanzu, Tunde Bakare da kuma tsofaffin manajan daraktocin matatar man Fatakwal, Ahmed Dikko Ibrahim Onoja, kamar yadda wata majiya ta shaida wa gidan Talabijin na Channels.

Sai dai duk kokarin jin ta bakin Kakakin EFCC, Dele Oyewale, hakan ya ci tura.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata