Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiManyan masu kudin Nijeriya su ne matsala wajen ci gaban Abuja -...

Manyan masu kudin Nijeriya su ne matsala wajen ci gaban Abuja – Wike

Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce manyan mutane da ke zaune a Abuja su ne babbar matsalar birnin saboda son rai da suke nunawa wajen biyan haraji.

Wike ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wasu sabin hanyoyi a Abuja, da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi don cika shekara biyu a kan karagar mulki.

Ministan ya ce manyan mutanen da ke zaune a Abuja ba sa son biyan haraji sai dai abin takaici suna biyan kudin haya bisa radin kansu a Landan da Amurka da sauran kasashen waje.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata