Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa an kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan wasu ‘yan asalin jihar su 12 a jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya ziyarci wadanda harin ya rutsa da su a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna.
Ya ce yana ci gaba da tattaunawa da gwamnan Filato Caleb Mutfwang da kuma shugaban kasa Bola Tinubu domin ganin an hukunta duk wadanda ke da hannu a harin.
