Jam’iyyar NRM mai mulki a kasar Uganda ta ce shugaban kasar Yoweri Museveni zai sake neman tsayawa takara a zaben da za a gudanar a farkon shekara mai zuwa.
Ana hasashen cewa shugaban mai shekaru 80 a duniya zai yi kokarin tsawaita mulkinsa na kusan shekaru 40 a kasar da ke gabashin Afirka.
‘Yan adawar kasar na ci gaba da fuskantar musgunawa gabanin babban zaben kasar da za a gudanar a watan Janairu, inda ake tsoratar da su da kuma garkame su.