By Salisu Ado Sulaiman
Rundunar sojin kasan Nijeriya ta jagoranci zaman sulhu tsakanin kabilun da ke rikici a jihar Taraba.
Kwamandan rundunar Operation Whirl Punch Brigadier Janar Kingsley Uwa wanda ya jagoranci sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu a karamar hukumar Gassol da ke jihar, ya nuna illolin da ke tattare da daukar doka a hannu ga jama’a.
Masu ruwa da tsaki da suka hadar da sarakunan gargajiya da sauran jagororin al’umma, sun halarci zaman sulhu da ya gudana a shalkwatar rundunar da ke Jalingo babban birnin jihar.
Wata sanarwa da sashen yada labarai na rundunar ya fitar, ta bayyana cewa akwai bukatar samun hadin kai daga dukkanin bangarori don ganin bayan matsalolin tsaro da ke addabar al’umma.