Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaYankin arewa ta tsakiya na kan gaba a neman mukamin kujerar shugabancin...

Yankin arewa ta tsakiya na kan gaba a neman mukamin kujerar shugabancin jam’iyyar APC

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa shiyyar Arewa, Bukar Dalori, ya hau matsayin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar har zuwa Disambar 2025.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Daniel Ihomun na ɓangaren Austin Agada da ke biyayya ga Sakataren Gwamantin tarayya George Akume da James Orgunga na ɓangaren Gwamna Hyacinth Alia, duk sun ce tsarin rabon mukamai na jam’iyyar ya bai wa Arewa ta Tsakiya dama.

A jihar Nasarawa kuwa, jiga-jigan jam’iyyar ta APC ne su ka nemi a bai wa tsohon gwamna Tanko Al-Makura shugabancin jam’iyyar, bisa hadin gwiwar shuwagabanni na yankin karkashin jagorancin Alhaji Saleh Zazzaga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata