Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaGuguwar Tinubu na shirin awon gaba da karin gwamnoni biyar da wasu...

Guguwar Tinubu na shirin awon gaba da karin gwamnoni biyar da wasu cikin jiga-jigan ‘yan Adawa a Nijeriya – Dr. Ijeoma Arodiogbu

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce akalla gwamnoni biyar na dab da sauya sheƙa zuwa cikinta, a wani yunƙuri da ke ƙara ɗaga ƙarfinta gabanin zaɓen 2027.

Mataimakin Shugaban APC na Kudu maso Gabas, Dr. Ijeoma Arodiogbu, ya ce sauya sheƙar ba jita-jita ba ne, domin sun kusa tabbata.

Wannan na biyo bayan shiga APC da Gwamnonin Akwa Ibom da Delta — Umo Eno da Sheriff Oborevwori suka yi tare da tsohon mataimakin dan takarar shugaban ƙasa na PDP, Ifeanyi Okowa, da wasu ‘yan majalisa.

Tuni rahotanni suka bayyana gwamnan Anambra, Charles Soludo, na jam’iyyar APGA, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, yayin da ake rade-radin wasu jiga-jigan NNPP da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Caleb Mutfwang na Filato za su marawa Tinubu baya a 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata