Tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa an samu zaman lafiya a jam’iyyar PDP ne sakamakon sabuwar amincewa da juna tsakanin shugabannin jam’iyyar da kuma jajircewa ga zaman lafiya da hadin kai.
Saraki, wanda ya jagoranci majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019, ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taron kwamitin zartaswa na jam’iyyar PDP karo na 100 da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar a Abuja.
Ya ce shugabannin jam’iyyar sun gane cewa hadin kai na da matukar muhimmanci idan har PDP na son ci gaba da zama babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya kamar yadda jaridar Premium Times ta ambato.
