Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaKwankwaso na da 'yancin shiga jam’iyyar APC kamar kowa – Felix Morka

Kwankwaso na da ‘yancin shiga jam’iyyar APC kamar kowa – Felix Morka

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na da ‘yancin yanke hukunci kan makomar siyasar sa, ciki har da shigowa jam’iyyar mai mulki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito sakataren yada labarai na APC na ƙasa, Felix Morka, na bayyana hakan a wata tattaunawa da Channels TV, inda ya ce Kwankwaso ɗan siyasa ne mai fikira kuma ɗaya daga cikin manyan a Najeriya da ke da hurumin zaɓar inda ya ke so a fagen siyasa.

Morka ya ce kofar APC a buɗe take ga duk wanda ke da ra’ayin jam’iyyar, ko daga wane mataki ne. inda ya ƙara da cewa har yanzu ba a fara wata tattaunawa a hukumance ba da Kwankwaso kan Shirin komawarsa APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata