DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma ta gana da manyan jami’an MDD da na Bankin raya Afirka AfDB don daukar matakai kan harkokin ilimi da talauci a yankin

-

 

Gwamnonin Arewa maso yamma da wakilan MDD

Da yake jawabi bayan kammala taron a Abuja, shugaban kungiyar, Gwamnan jihar Katsina,Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa sun amince su ba da fifiko wajen wajen kare al’umma, bayar da ilimi da samar da abinci.

Ya bayyana cewa gwamnan Kaduna Uba Sani dana Zamfara Dauda Lawal ,Sokoto Ahmed Aliyu,Jigawa Umar Namadi sun halarci taron, wanda suka samu bayanai daga mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed da Kodinetan Majalisar Dinkin Duniya, Malick Fall,akan ci gaba tare da shirye shirye daban daban da karfafa hadin gwiwa tsakanin MDD da yankin.

Ya kuma bayyana cewa tattaunawa da bankin na AfDB ya mayar da hankali ne kan shirin bunkasa noma a Nijeriya wanda ya shafi jihohin Arewa maso Yamma.

Ya kara da cewa aiwatar da wannan shiri, zai kawo ci gaban aikin noma tare da inganta rayuwar al’ummar da ke yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu ‘yan jarida uku na Radio Sahara da ke jihar Agadez

Rahotanni daga gidan Radio Sahara Fm da ke jihar Agadez sun tabbatar da kama wasu 'yan jaridar gidan radiyon guda uku da suka hada da...

Majalisar wakilan Nijeriya ta ba gwamnonin Benue da Zamfara da shugabannin majalisunsu su wa’adin mako daya su gaggauta bayyana a gaban kwamitinta

Majalisar wakilan Nijeriya ta ba gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, da na jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da shugabannin majalisun dokokin jihunsu wa’adin mako guda...

Mafi Shahara