Gwamnatin Jihar Sokoto ta bukaci shugaban ‘yan bindiga Bello Turji da ya nuna cikakkiyar aniyyarsa ta zaman lafiya ta hanyar sakin dukkan mutanen da ke hannunsa tare da dakatar da hare-hare a karkara.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Sokoto.
Wannan kira na zuwa ne bayan da wani sautin murya da ake zargin na Bello Turji ne ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ya nuna shirin shiga tattaunawa da kuma kiran sauran shugabannin ‘yan bindiga da su rungumi zaman lafiya.
