Hukumar lura da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da guguwa daga Litinin zuwa Laraba a sassa daban-daban na Najeriya.
A sanarwar da ta fitar a Abuja, NiMet ta ce akwai yiyuwar ruwan sama da guguwa a safiyar Litinin a Taraba da Adamawa, da kuma daga bisani a Zamfara, Kebbi, Kaduna da sauran yankuna.
A Arewa ta tsakiya, ana sa ran gizagizai da hasken rana a safiya sannan daga bisani a samu ruwan sama da guguwa a FCT, Kogi, Niger, Benue, Filato da Nasarawa.
A Kudu, za a fara da ruwan sama a Lagos, Ogun, Ondo, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Delta da Bayelsa, sannan daga baya a ci gaba da ruwan sama a Oyo, Ekiti, Osun, Edo da sauran jihohin kudu.
A ranar Talata kuma, za a fara da hasken rana a Arewa, sai daga baya a samu guguwa da ruwan sama a Bauchi, Taraba, Kaduna, Kebbi, Katsina, Kano da Adamawa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ambato.
