Shugaban jam’iyyar YPP na kasa, Bishop Amakiri, ya caccaki hadakar jam’iyyun adawa da suka dauki ADC a matsayin dandamalin su na zaben 2027, yana mai cewa kusan kashi 85% na shugabannin hadakar sun gaza a mukaman da suka rike a baya.
A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Amakiri ya bayyana cewa yawancin ‘yan hadakar sun taba rike madafun iko amma sun ci amanar ‘yan kasa, don haka ba su da kwarin gwiwar kawo sauyi na gaskiyar da suke zumundin kawowa.
Inda ya bayyana gamayyar a matsayin hadakar da ke ba da fifiko ga bukatar kashin kai madadin al’ummar su.
