Monday, April 6, 2026
HomeLabarai‘Yan sandan jihar Anambara sun kama matashi mai shekaru 25 dauke da...

‘Yan sandan jihar Anambara sun kama matashi mai shekaru 25 dauke da sassan jikin wata mace a jihar

Rundunar ‘yan sanda a jihar Anambra ta kama wani matashi mai suna Samuel Eze, mai shekaru 25, dauke da sassan jikin wata mace a unguwar Awada, Obosi.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, SP Tochukwu Ikenga, ya ce Eze ya shiga hannu ne a ranar 6 ga Yuli yayin sintiri da hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda da na kungiyar vigilante.

Mujallar chronicles ta ce an kai sassan jikin da aka gano zuwa dakin ajiye gawa, yayin da ake ci gaba da bincike.

Haka zalika, a ranar 4 ga Yuli, rundunar ta ceto wani direba da aka sace a Enugwu Ukwu, inda aka kama mutum uku da ake zargi tare da kwato motar dauke da kaya na Naira miliyan 9 da dubu 500 a samemen da ta gudanar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata