Jam’iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom na neman takara da sha’awar zama ‘yan takara domin zaben cike gurbi na Majalisar Tarayya da za a gudanar a ranar 16 ga Agusta, a jihohi 12.
Zaben wanda ke nufin cike guraben da aka rasa sakamakon rasuwa ko murabus din wasu ‘yan majalisa da suka tsaya takarar wasu mukaman wakilci a kasar.
A wani jawabi da ya yi bayan karbar fom dinsa, dan takarar kujerar Ovia South-West/North-East a Jihar Edo, Oscar Aghedo, ya ce zai bai wa yankinsa wakilci nagari musamman ta fannin ci gaban ababen more rayuwa.
Inda ya bukaci kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC) da su tabbatar da sahihin zabe a ranar 19 ga Yuli, kamar yadda rahoton jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
