Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiMalamai 915,913 ke kula da dalibai sama da miliyan 31 a makarantun...

Malamai 915,913 ke kula da dalibai sama da miliyan 31 a makarantun firamare na Nijeriya – Hukumar ilmi UBE

Bayanan da aka samu daga Hukumar Ilimi ta Nijeriya UBE, ta nuna yadda malamai a jihohi da babban birnin tarayya Abuja ke fama da rashin biyan mafi karancin albashi, da rashin yanayin aiki mai kyau da dai sauransu.

A kwanakin baya ne malaman birnin tarayya suka fara yajin aikin, biyo bayan gaza wajen biyansu mafi karancin albashi da shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a bara.

A shekarar 2024, jaridar PUNCH ta ruwaito yadda jihohi 18 na tarayya suka ƙi daukar malamai tsawon shekaru biyar, daga 2019 zuwa 2024.

Hakazalika, hukumar rijistar malamai ta Nijeriya ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin karancin kwararrun malamai a kasar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata