Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya soki sabuwar hadakar jam’iyyu da aka kafa kwanan nan, yana mai bayyana wadanda suka kirkiro da ita a matsayin fusatattun da suka rasa mulki.
Dikko Radda ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Talata, inda ya ce: “Mu fadi gaskiya. Lokacin ya wuce da za a ci gaba da yaudarar ‘yan Najeriya. Wadanda ke ihu a yau, su suka yi mulki jiya. Mun san tarihin kowa, mun san abin da suka aikata a lokacin da suke cikin gwamnati.”
Sabuwar hadakar jam’iyyu ta amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin da za su kalubalanci gwamnatin APC ta Shugaba Tinubu.
Gwamnan Katsina ya caccaki hadakar tare da dora ayar tambaya sahihancin manufarta da kuma gaskiyar dalilin kafuwarta.
