Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiJami’o’in Nijeriya sun sanya maki 150 a jarabawar JAMB ta 2025 a...

Jami’o’in Nijeriya sun sanya maki 150 a jarabawar JAMB ta 2025 a matsayin ka’idar samun gurbin karatu

Shugabannin jami’o’in Nijeriya sun amince da maki 150 a matsayin mafi karanci da ɗalibi zai iya samu domin samun gurbin karatu a jami’a a shekarar 2025, yayin taron tsarin karɓar ɗalibai da Hukumar JAMB ta shirya a ranar Talata.

Wannan yana nufin cewa ba wata jami’a da za a yarda ta karɓi ɗalibin da ya kasa samun maki 150 a jarrabawar JAMB ta 2025.

Sai dai wasu jami’o’i kamar su University of Ibadan, Pan-Atlantic University, da University of Lagos sun ɗaga ƙa’idar su zuwa maki 200, yayin da wasu sabbin jami’o’in masu zaman kansu suka ba da shawarar amfani da maki 120.

A nasa bangaren, Shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede, ya ba da shawarar a kayyade maki 160 a matsayin ƙa’ida.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata