Babbar Kotun Abuja ta sanya ranar 17 ga Yuli domin yanke hukunci kan bukatar da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya shigar don neman izinin fita kasar waje domin neman lafiya.
Mai shari’a Maryanne Anenih ce ta bayyana ranar, bayan sauraron hujjoji daga bangarorin masu kara da masu kariya a zaman kotun da aka yi ranar Talata.
Yahaya Bello na fuskantar shari’a ne tare da wani Umar Oricha, tsohon daraktan fadar gwamnatin Kogi da wani Abdulsalami Hudu kan tuhume-tuhume 16 da hukumar EFCC ke yi musu, ciki har da karkatar da dukiyar al’umma da ta kai Naira biliyan 110.4 da kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
