Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAPCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda...

APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati

Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi ta sanar da dawo da Kabir Sani-Giant, mai ba Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin wutar lantarki da siyasa, zuwa kujerarsa nan take.

An dakatar da Kabir Sani-Giant a ranar 28 ga Fabrairu, 2025, bisa zargin kawo maciji fadar gwamnati a ranar 8 ga watan nan, da nufin tsoratar da manyan baki, jami’an gwamnati.

A wata sanarwa da Shugaban APC na Jihar Kebbi, Muhammad Kana-Zuru, ya fitar a ranar Litinin daga Birnin Kebbi, ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jiha ya karanta kuma ya yi la’akari da takardar afuwar da Sani-Giant ya rubuta, kuma ya yanke shawarar janye dakatarwar da aka yi masa.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

2 COMMENTS

  1. I am not sure where you’re getting your information, but great topic.
    I needs to spend some time learning more or understanding more.
    Thanks for fantastic information I was looking for this information for my mission.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata