Kamfanin matatar mai ta Dangote ya bayyana cewa daga karshen watan Disamba, zai dakatar da shigowa da danyen mai daga kasashen waje, tare da komawa sayen danyen mai daga cikin gida Najeriya.
A cewar rahoton Bloomberg da Channels TV suka wallafa, Mataimakin Shugaban Kamfanin Dangote kuma mai kula da Matatar Man, Devakumar Edwin, ya bayyana cewa yarjejeniyar da ke tsakanin kamfanin da masu samar da danyen mai daga kasashen ketare za ta kare a watan Disamba.
Edwin ya ce da zarar wannan mataki ya fara aiki, matatar za ta daina dogaro da kasashen waje kamar Brazil, Angola, Ghana da Guinea wajen samun danyen mai, domin maye gurbinsu da man da ake hakowa a cikin Najeriya.
