Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi ajalin ’yan bindiga 30 a wani samame da suka kai a kauyukan Kadisau, Raudama da Sabon Layi a karamar hukumar Faskari a ranar 8 ga watan Yulin, 2025.
Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Dr. Nasir Mua’zu, ya ce Dakarun hadin gwiwa na rundunonin ’yan sanda, sojoji da sojin sama sun yi artabu da ’yan bindigar da suka kai hari, inda aka kawo karshen su ta hanyar luguden wuta daga sama da bindiga.
Sai dai an rasa jami’an tsaro uku da wani dan kauyen Kadisau, Yayin da wasu biyu suka jikkata a harin.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce Gwamna Dikko Radda ya sha alwashin ci gaba da yaki da ’yan ta’adda tare da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Allah ya kawo mana karshan tashe tashen hankula a kasar mu nigeria ya taimaki jami’an tsaron mu