Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya karyata jita-jitar da ke cewa zai fice daga jam’iyyar PDP, yana mai jaddada cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar ne kuma ba shi da wani shirin sauya sheƙa zuwa APC ko ADC.
Jam’iyyar ADC dai na daga cikin sabbin dandamalin da hadakar jam’iyyun adawa suka ɗauka a matsayin mafita gabanin zaɓen 2027.
Da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Laraba, Lawal ya bayyana rahoton a matsayin jita-jita kawai.
Rahoton jaridar Punch ya ruwaito gwamnan na cewa bai nemi wata kariya ta siyasa daga jam’iyyar APC ba, duk da irin matsin lambar da wasu ’yan adawa ke yi masa a jiharsa.
Ya kuma ce waɗanda ke ƙoƙarin kawo masa cikas a yau su ne irin su tsoffin Gwamnonin jihar Sani Yerima da Bello Matawalle, waɗanda suka sha kaye a zaɓen gwamna na 2023.
