Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaGwamnatin Abacha ce ta bai wa kamfanin malabu rijistar mai ta OPL...

Gwamnatin Abacha ce ta bai wa kamfanin malabu rijistar mai ta OPL 245 a shekarar 1998 – Jonathan

Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa tsohon Antoni Janar na ƙasa Mohammed Adoke ya fuskanci farauta ta duniya sakamakon shari’ar rijistar mai ta OPL 245.

Jonathan ya fadi haka ne a Abuja yayin ƙaddamar da littafin tarihin Adoke mai take: “OPL 245: Inside Story of the $1.3 Billion Nigerian Oil Block.”

A cewarsa, littafin ya bayyana gaskiyar lamari, kuma ya nuna yadda gwamnatin da ta gaje shi a 2015 ta fara farautar manyan jami’ansa, musamman Adoke, wanda ya kasance a sahun gaba a harkar doka a lokacin mulkinsa.

OPL 245 dai rijista ce ta hakar mai da gwamnatin Sani Abacha ta bai wa kamfanin Malabu Oil and Gas a 1998 kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata