Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaAdalci shi ne a kyale Kudu ta ci gaba da mulki a...

Adalci shi ne a kyale Kudu ta ci gaba da mulki a 2027 – Minista Hannatu Musawa

Ministar harkokin al’adu, da tattalin arzikin kirkira, Hannatu Musawa, ta bayyana cewa ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da kasancewa a yankin Kudu a zaben 2027 domin tabbatar da adalci da daidaito a rabon mulki.

Ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a tashar Channels TV ranar Juma’a, tana mai cewa ko da yake tsarin karba-karba tsakanin Arewa da Kudu ba ya cikin kundin tsarin mulki, bai kamata a karya shi ba.

Musawa ta ce tun da Shugaba Bola Tinubu daga Kudu maso Yamma ya karbi mulki daga Muhammadu Buhari na Arewa maso Yamma, to mulkin na bukatar ci gaba da kasancewa a Kudu a zango na gaba.

Wannan ra’ayi nata na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke kira ga sabuwar kawancen jam’iyyu karkashin ADC da su tsaida dan takara daga Arewa a zaben shugaban kasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata