Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiKotu ta tsare mutane 20 da ake zargi da ajalin 'yan daurin...

Kotu ta tsare mutane 20 da ake zargi da ajalin ‘yan daurin aure a Mangu ta jihar Plateau

Kotun Majistare mai lamba 10 da ke Jos, ta bayar da umarnin tsare mutane 20 da ake zargi da ajalin matafiya 13 a wani farmaki da aka kai musu a hanyar su ta zuwa daurin aure a kauyen Kwa, na karamar hukumar Qua’an Pan, ta Jihar Filato.

Mutanen da suka hada da maza da mata da yara, sun taso ne daga Basawa, Sabon Gari a Jihar Kaduna, a cikin mota mai daukar fasinja 18, lokacin da suka fada hannun wasu da ake zargin matasa ne a yankin Mangun.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce a ranar Alhamis, ne rundunar ‘yan sanda ta jihar ta gurfanar da mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan, gaban kotu.

Sai dai lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Garba Pwol, ya bayyana cewa akwai yara ‘yan shekara 13 da 17 a cikin wadanda ake tuhuma, wanda hakan ya sa kotu ta bukaci a cire su daga cikin karar tare da gyara tuhumar kafin cigaba da shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata