Garba Shehu, Tsohon mai magana da yawun Buhari, ya bayyana a littafinsa cewa ya kirkiri labarin beraye sun lalata ofishin shugaban kasa a 2017 don karkatar da hankalin jama’a daga tambayoyin da ake yi kan lafiyar Buhari bayan dawowarsa daga jinya a Birtaniya.
Ya ce labarin ya samo asali ne daga zancen wani kebul da ya lalace a ofishin, wanda aka danganta da beraye.
Labarin ya bazu a duniya, wanda kuma ya taimaka wajen rage matsin lamba kan tuhumar yanayin lafiyar shugaban kasar a wancan lokacin kamar yadda rahoton jaridar Punch ya tabbatar.

OK