Fadar shugaban kasa ta karyata rade-radin da ke danganta jawabin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da rikicin siyasa na baya-bayan nan a Jihar Ribas da ya shafi Gwamna Siminalayi Fubara da Shugaba Bola Tinubu.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba kasa kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana rahotannin kafafen yada labarai da ke alakanta Shettima da lamarin a matsayin kuskure mai hatsarin kawo rarrabuwar kai a kasa.
Nkwocha ya ce jawabin Shettima da aka yi a taron kaddamar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block” da tsohon Atoni janar na kasa, Mohammed Bello Adoke, ya rubuta, ya ta’allaka ne da wani tarihi da ya faru a lokacin gwamnatin Jonathan, inda aka yi yunkurin cire Shettima daga mukaminsa na Gwamnan Borno a lokacin da Boko Haram ke ta’asa a jihar kamar yadda jaridar Punch ta ambato.
