Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a garin Jargaba da ke karamar hukumar Bakori, ta Jihar Katsina, inda suka yi ajalin mutum shida tare da sace wasu biyu da kuma jikkata yara biyu.
Rahoton jaridar Punch ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis lokacin da maharan da dama suka afka garin inda suka nufi wajen zaman maza suka bude wuta kai tsaye, suka yi ajalin mutum shida da ke zaune suna hira.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutum biyu sun rasu nan take, yayin da karin hudu daga cikin wadanda suka jikkata suka rasu washegari.
