Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana matuƙar damuwarta kan sammacin kama Hamdiyya Sidi Sharif da kotun Majistare ta Wurno da ke zamanta a unguwar Gwiwa cikin garin Sokoto ta bayar a ranar 10 ga Yuli.
A cewar kungiyar, sammacin kama Hamdiyya ya ci karo da ka’idojin adalci da damar kare kai, duba da cewa ta gaza halartar zaman kotun na 9 ga Yuli ne sakamakon jinya da take yi bayan ta sha wahala a hannun masu garkuwa da ita.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafintsa na Facebook, Amnesty International ta yi kira da a janye sammacin kama Hamdiyya har zuwa lokacin da za a saurari ƙudurin da lauyoyinta suka shigar tun ranar 19 ga Yuni, wanda ke neman kotu ta ci gaba da shari’a ba tare da ta halarci zaman ba.
Hamdiyya na fuskantar shari’a bisa zargin amfani da “kalaman batanci ko cin mutunci” da kuma “tayar da husuma”, sakamakon suka da ta yi wa Gwamna Ahmed Aliyu dangane da matsalar tsaro a yankin gabashin Sokoto.

Wannan shi yake nuna cewar mafi yawan Alkalan Nigeria basu da Adalci wajen gudanar da Shari’a. Musamman idan ta danganci tsakanin mai Hannu da Shuni da kuma Talaka, Allah gatan Talaka. Ya Ubangiji Allah ka kawo mana Mafita dangane da Rashin Adalcin Shuwagannin Kasar nan tamu…
Ameen summa ameen
Wani abu sai kasa ta nigeria mai rike da ak47 in an kama shi yana da yanci fuskantar shari’a amma talaka maras taro sai da ahu sai salati da sallal lami ya allah ka kawo wa talakan kasata a gajinka
Allah sarki talakan kasata