Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiMa'aikatan lafiya 15,421 suka bar Nijeriya zuwa Birtaniya cikin shekara takwas -...

Ma’aikatan lafiya 15,421 suka bar Nijeriya zuwa Birtaniya cikin shekara takwas – Inji wani rahoto

Akalla ma’aikatan lafiya da ungozomomi 15,421 da suka samu horo a Nijeriya, aka ba lasisin yin aiki a Birtaniya tsakanin shekarar 2017 da 31 ga Maris, 2025.

Wannan kididdiga ta fito ne daga sabbin bayanai da hukumar kula da ma’aikatan lafiya da ungozomomi ta Birtaniya ta fitar.

A ranar 30 ga Satumba, 2024, adadin ya kai 14,815, amma ya karu zuwa 15,421 a 31 ga Maris, 2025, abin da ke nuna karin kashi 4.1 cikin ɗari.

Najeriya ce ta uku a jerin ƙasashen da suka fi yawan ma’aikatan lafiya da suka yi hijira zuwa Birtaniya, bayan Philippines da India.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata