Majalisar Dattawa ta bayyana cewa matsalolin tsaro da suka haɗa da ‘yan bindiga, ta’addanci da garkuwa da mutane da suka addabi Nijeriya a baya, yanzu suna ci gaba da raguwa.
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.
Adaramodu, wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin yaɗa labarai na majalisar, ya ce rundunar soji ta yi kokari matuƙa wajen yaki da rashin tsaro.
Ya ce, “Dalilin da ya sa dakarun soji suka yi nasara shi ne domin majalisa ta tabbatar da cewa an yi kasafin kuɗi yadda ya kamata don samar da makamai, alburusai da kuma kula da jin daɗin sojoji.
Adaramodu ya ce wannan ne ya sa sojoji ke ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga kuma barazanar tsaro ta takaita ne a wasu jihohi kaɗan kuma duk da haka ana dakile su.
Kokarin majalisar dattawa ya sa matsalar tsaro ta yi sauki a Nijeriya – Inji Sanata Adaramodu
Recent Comments
on Gwamnatin Tinubu za ta fara ba da rancen maras kuɗin ruwa ga manoma da masu ƙananan sana’o’i – GEEP
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030
on Jaridar Daily Trust ta gano dalilai uku da suka sa Ganduje ya ajiye mukamin shugabancin APC na kasa
on Peter Obi ya sake jaddada bukatar kafa tsarin wa’adin shekara 5 kacal ga shugaban ƙasa a Najeriya
on Cire tsoffin ‘yan sanda daga daga tsarin Contributory Pension Scheme ya fi karfina – IGP Egbetokun
on Gwamnatin Nijeriya ta ɗage buɗe shafin neman aiki na Immigration, Civil Defence da sauran hukumomi
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3
on APCn jihar Kebbi ta yafe wa hadimin gwamna da aka dakatar saboda ya zo da maciji a fadar gwamnati
on An karkatar da Naira Bilyan 71.2 daga cikin Bilyan 100 na bashin dalibai a Nijeriya – Hukumar ICPC
on Gwamna Abba Gida Gida ya zabi tsohon shugaban ma’aikatansa da wasu mutum 5 a matsayin kwamishinoni
on Nijeriya za ta zama jagorar kasuwar halal ta duniya mai jarin Dala bilyan Dubu 7 – Kashim Shettima
