Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAn rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da bin umarnin hutun da gwamnatin Najeriya ta ayyana, bayan rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X dinsu a ranar Litinin.’

Sanarwar ta ce: “Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja da na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin bin hutun da gwamnatin Najeriya ta ayyana don girmama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.”

“Dukkanin jadawalin ganawar neman visa da aka tsara a wannan rana za a dage su zuwa wani lokaci na gaba,” in ji sanarwar.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata