DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sojoji na dab da yi wa Bello Turji ‘Ƙofar Raggo’ – Rundunar sojin Nijeriya

-

Rundunar sojin Najeriya ta ce nan ba dadewa ba ƙasurgumin dan ta’adda Bello Turji zai zo hannu.
Jami’in yada labaran rundunar ta operation Fansar Yamma Laftanal Kanal Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da makaman da rundunar ta ƙwace daga ‘yan bindiga a karamar hukumar Kaura -Namoda dake jihar Zamfara.
Abubakar ya ce Turji na cigaba da wasan buya tsakaninsa da rundunar, sai dai ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya rundunar za ta kamo shi.
Jami’in ya yaba tare da godewa al’umma bisa hadin kai da bayanan sirri da suke bai wa rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wadanda suka yi garkuwa da ‘yan Mauludi 28 a jihar Plateau na neman kudin fansa N1.5m kan kowane mutum

‘Yan bindiga da ake zargin sace mutane 28 a ƙauyen Zak, karamar hukumar Wase, Bashar, jihar Filato, sun tuntubi iyalan wadanda suka yi garkuwa da...

Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar dokokin haraji

Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji, tana mai cewa rikice-rikicen da suka...

Mafi Shahara