Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiHarin ‘yan bindiga a Zamfara ya yi ajalin mutum 9, tare da...

Harin ‘yan bindiga a Zamfara ya yi ajalin mutum 9, tare da sace wasu da dama

Aƙalla mutane tara aka tabbatar sun rasu, yayin da mata da yara da dama aka yi garkuwa da su a wani hari da ’yan bindiga suka kai a Jihar Zamfara, a Arewa maso Yammacin Najeriya, ranar Juma’a.

Wakilin yankin, Hon. Hamisu Faru, ya shaida wa kafar yada labarai ta Reuters cewa fiye da mutane 100 aka sace, inda ya ce “a halin yanzu ma suna ci gaba da bin gida-gida suna sace jama’a.”

Shugaban karamar hukumar Talata Mafara, Yahaya Yari Abubakar, ya tabbatar wa AFP cewa an salwantar da ran mutane 9, kana an sace wasu 15 a harin da aka kai kauyen Jangebe.

Wani mazaunin kauyen, Abu Zaki, ya bayyana cewa cikin wadanda suka mutu akwai shugaban matasan sa-kai na kauyen da wasu mutum biyar daga cikinsu, da kuma wasu mazauna kauyen guda uku.

Jihar Zamfara na daga cikin wuraren da ’yan bindiga ke addabar mutane, inda suke satar mutane, su yi ajalin wasu, tare da hana mutane zirga-zirga cikin aminci a wasu sassan Arewa maso Yamma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata