Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiTCN ta koka kan yawaitar lalata turakun lantarki a Kudu Maso Gabashin...

TCN ta koka kan yawaitar lalata turakun lantarki a Kudu Maso Gabashin Nijeriya

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya nuna damuwa kan yawaitar lalata kayayyakin wuta da ake yi a wasu yankunan Kudu maso Gabas, musamman a Agbogugu da Ihe na karamar hukumar Awgu a jihar Enugu.

Shugaban TCN na yankin Enugu, Dr. Thomas Inugonum, ya ce matsalar tana janyo asarar kayan aiki da katse wuta, yayin da kamfanonin rarraba wuta (DISCOs) ke jingina gazawarsu da lalata layukan lantarki.

Rahoton jaridar The Nation yace an bukaci shugabannin gargajiya da matasa su taimaka wajen kare kayayyakin wuta, yana mai cewa TCN tana da isasshiyar wuta a tashoshinta, amma DISCOs na gaza rarrabawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata