Kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da ke neman a mayar masa da fasfonsa domin tafiya ƙasa Birtaniya don neman lafiya.
Alƙalin da ke sauraron shari’ar, Emeka Nwite, ya ce Bello bai gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su gamsar da kotu cewa lallai ya cancanci tafiyar ba.
Wannan hukuncin ya zo ne kwanaki bayan wata kotu a Abuja da ke sauraron karar zargin karkatar da Naira biliyan 110 na cin hanci, ta kuma ƙi buƙatar makamanciyar hakan.
Rahoton Premium Times ya ruwaito hukumar EFCC da ke karar Bello a kotunan biyu ta ce akwai barazanar Bellon ya tserewa daga ƙasar, kasancewar ya ƙi bayyana a gaban kotu sau da dama, har sai da aka matsa masa kafin ya miƙa kansa.
Lauyan Bello, Joseph Daudu (SAN), ya ce wanda yake karewa yana fama da hawan jini tsawon shekaru 15.
Ya kuma gabatar da rahoton lafiya daga likita a matsayin hujja, amma EFCC ta ce wannan rahoto ba a sa hannu a kansa ba, don haka bai da wata ƙima a idon doka.
