Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci a dauki tsauraran matakai kan mazajen da ke dukan matansu da masu haikewa kananan yara a jihar Kano.
Rahoton jaridar Daily Trust yace sarkin ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke Kano yayin da yake karbar tawagar cibiyar dRPC da CICID ta Jami’ar Bayero, inda ya ce Musulunci ya girmama mata fiye da kowace addini.
Ya ce masu dukan mata ba su da hujjar yin hakan a addini, kuma ba su da ladabi ga koyarwar Annabi (SAW).
Ya kuma bukaci a dawo da amfani da daftarin dokar kula da iyali ta jihar Kano domin yakar cin zarafin mata, yana mai jan hankalin sarakunan gargajiya su saka hannu wajen dakile lamarin.
