Wednesday, April 8, 2026
HomeSiyasaAn taba yi min kyautar gidan Naira milyan 120 amma na ki...

An taba yi min kyautar gidan Naira milyan 120 amma na ki karba – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana yadda ya ƙi karɓar kyautar gida da darajarsa ta kai Naira miliyan 120 lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi yayin cika shekarunsa 64, jaridar Daily Trsut ta ruwaito Obi ya ce lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 50 ne aka yi masa tayin gidan, amma ya nemi a mayar da kuɗin don gina ajujuwa a makarantu a Agulu, Ekwulobia da Abatete.

Haka kuma, ya ce wasu da suka ware Naira miliyan 20 don bikin hadin kai, ya roƙe su su sayi kwamfutoci ga makarantu.

Daga baya sun bayar da kwamfutoci 200 da aka raba wa dalibai a faɗin jihar.

Obi ya jaddada bukatar a karkatar da dukiyar gwamnati zuwa aikin al’umma, yana mai cewa ya fi son amfani da irin waɗannan damarmaki wajen inganta rayuwar talakawa, ba taron biki ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata