Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnan Benue Hyacinth Alia ya soke majalisar zartarwar jihar

Gwamnan Benue Hyacinth Alia ya soke majalisar zartarwar jihar

Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya rushe majalisar zartarwar jiharsa gaba ɗaya, inda ya sallami dukkan kwamishinoni da kuma Shugaban Ma’aikata na fadar gwamnati.

Sanarwar hakan ta fito ne daga kakakin gwamnan, Tersoo Kula, wanda ya bayyana cewa gwamnan ya sanar da wannan matakin ne a ƙarshen zaman majalisar zartarwa na 12 da aka gudanar a shekarar 2025.

Gwamna Alia ya umurci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar mulki ga sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu nan da nan ba tare da jinkiri ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata